FAƊUWAR ƊAN TA'ADDA DULLU DA BUNƘASAR BELLO TURJI

Faɗuwar ɗan ta'adda Dullu da bunƙasar ƙungiyar Bello Turji.

Aliyu Samba

Dullu, sanannen dan fashin daji ne daga kauyen Maniya dake karamar hukumar Shinkafi a jihar Zamfara. An kashe shi ne a jiya bayan sun yi arangama da yan kungiyar Bello Turji, shahararren shugaban ‘yan ta'adda masu fashi da makami a karamar hukumar Shinkafi ta Zamfara.


Turji ya kashe Dullu ne saboda ya kaiwa yaran Turji hari a Ƙauyen Jangeru sannan ya kwashe sama da shanu 100 da suka sato daga Maradun da Bungudu duk a jihar Zamfara. 
Kafin arangamar, Turji ya gayyaci manyan ‘yan bindiga uku da suka haɗa da; Boka, Atarwatse daga Kagara (Jihar Neja) da kuma Standard daga Zurmi (Jihar Zamfara) don hadin gwiwa da kai wa ga Nasara akan Dullu.

Majiyoyi sun bayyana cewa sun kai harin ne akan babura sama da 300, kuma kowanne babur na dauke da mayaka uku inda suka nufi Maniya, sansanin da Dullu da yaran sa ke kai wa mutane hari. Sun ƙone wurare da dama a kauyen na Maniya da wasu ababen fashewa daban-daban, sannan suka kashe Dullu tare da kwashe daruruwan dabbobi da suka hada da shanu, buhu 10 dauke da kudi, kayan abinci da sabbin babura.

Bayan shafe sa'o'i uku ana arangama, Turji ya ayyana mayakan Dullu a matsayin kadarorinsa tare da ba da umurnin su mika dukkan makaman su da sauran kayan aiki. Daga baya Turji ya zagaya zuwa wasu al'ummar Fulani inda marigayi Dullu ya yi kaurin suna kamar Birnin Yero, ya kwashe shanunsu ya kona al'ummar yankin, sannan ya koma garin Badarawa wata al'ummar da ke karkashin ikon Dullu ya kashe yaransa sannan ya kwashe musu dukiya. 

Wannan arangama ta ƙarawa dan ta'adda Bello Turji ƙarfi a tsakanin yan ta'addan dake yankin sa, kuma alamu na ƙara bayyana cewa a yanzu shine ɗan ta'adda mafi ƙarfin iko a yankin Shinkafi dake jihar Zamfara.

📷 Twitter/ Edress4P

#Gwarzo

Comments

Popular posts from this blog

SABON RIKICI YA KUNNO KAI KAN SHUGABANCI A JAM'IYYAR APC