Kodai Dalibai Su Hadu Su Tilastawa Gwamnatin Tarayya Da ASUU Akoma, Ko Atafi A Haka Babu Lokacin Dawowa – Bukarti



Daga: Fahad Kabir Mai Tata

Wani lauya mai zaman kansa a Nigeria kuma mazaunin Burtaniya a yanzu haka, Audu Bulama Bukarti, ya kalubalancin kungiyar malaman Jami’o,i ASUU da sauran hukumomin harma da gwamnatin tarayya.

Bukarti ya ce a duk kasashen Duniya Nigeria ce kadai kasar da suke iya rufe makarantun su na jami’a wata da watanni, kuma ayi shiru babu wani mai yin motsi.
“Ba ga yan siyasar, haka malaman jami’o,in dama hukumomi.
“Babu wata kasa da tasan me take yi wacce zata bari ana irin wannan abu, tayaya zamu sami cigaba a irin wannan yanayi ?


 
“To kodai dalibai wanda abun ya shafa su fara hada kan su damin su tursasa gwamnatin tarayya da ASUU a dawo, ko kuma abun ya cigaba har sai abun da aka gani” acewar sa.

Audu wanda ya yi wannan bayani a ranar Laraba akan shafin sa na sada zumunta.


 
Tun a ranar 14 ga watan Maris na shekarar da muke ciki ne ASUU ta tsindima yajin aiki, wanda ta shafe tsawon watanni biyu tana yi.

Kazalika bayan zaman samar da masalaha da akaita yi a tsakanin su da gwamnati, ba’a sami dai daito ba wanda yasa suka zarce da yin yajin aikin zuwa watanni uku.
#Gwarzo

Comments

Popular posts from this blog

SABON RIKICI YA KUNNO KAI KAN SHUGABANCI A JAM'IYYAR APC