Zaratan NNPP a cigaba da fadar alherin da Madugu ya samar ga alumma. Sakonku yana isa ko ina a fadin kasar nan. Mutumin da yayi kokarin bawa talaka ilmi ai shine masoyinsa. Duk wanda ya ji zancennan bai masa dadi ba, sai shima ya bada himma wajen fadar alherin da dantakarar jamiyyarsa ya samar ga alumma. Jama'a kuma suyi masa alkalanci. 

Kwankwaso nan har baya mulki bai daina daukar nauyin karatun matasa da suka cancanta ba. Babu dangin iya babu na Baba, sai dai kawai kishin ganin alumma ta cigaba. Idan fitsari banza ne kaza tayi mana. 

Duk yan takarar nan babu wanda Allah bai bawa wata dama a baya ba da zai hidimtawa al'umma. Babu laifi domin an nemi a kawo alkaluman cigaban da suka samar a madafun ikon da Allah ya yassare musu a baya. Ai daga na gaba akan ga zurfin ruwa. Sai a lullube mana mutum kawai mu zabe shi bamu auna shi a sikeli ba? An sha mu mun warke. Juma'ar da zatayi kyau tun daga laraba ake gane ta. 

A mikowa Alaramma kayan marmari ya dan taba kafin a rufe tamsirin yau.

Comments

Popular posts from this blog

SABON RIKICI YA KUNNO KAI KAN SHUGABANCI A JAM'IYYAR APC